Difference between revisions 31492 and 31493 on hawiki

== Tarihi ==


Ita dai '''Kambodiya''' wata ƙasa ce da ke kudu maso gabashin [[Asiya]] kuma ta na da jama'a da yawansu ya haura miliyan 13. Sunan babban birnin ƙasar [[Phnom Penh]]. Kambodiya ta samo asali ne daga daular Hindu da Buddha, wadda ta mulki yankunan [[Indonesiya]] da [[Sin|China]] tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 14.

Yawancin ‘yan ƙasar Kambodiya mabiya addinin Buddha ne, amma kuma akwai musulmi da dama da chinese ‘yan asalin



  ƙasar, da yan asalin ƙasar [[Vietnam]] da kuma yan tsirarun yarurruka da ke zaune akan tsaunuka.

Ƙasar Kambodiya na maƙwabtaka da ƙasashen [[Thailand]] a yammaci da kuma yamma maso arewa, [[Laos]] a arewa maso gabas da Vietnam a gabas da kudu maso gabas. A kudu tana fuskantar kogin Thailand.

(contracted; show full)

Masana'antun ƙasar Kambodiya dai sune na sutura, yawon shaƙatawa da kuma gine-gine. A shekara ta 2007, yawan baƙin da suka ziyarci ƙasar daga ƙasashen waje ya haura miliyan biyu. An gano mai da albarkatun ƙasa a ƙarkashin ruwan dake zagaye da ƙasar a shekara ta 2005, kuma idan aka fara zaƙulo waɗannan albarkatun ƙasa a shekara ta 2011, to ana ganin cewa kuɗin shigan da za a riƙa samu daga Man zai haɓaka arziƙin ƙasar ta Kambodiya

{{Asiya}}

[[Category:Asiya]]