Revision 23126 of "Kambodiya" on hawiki== Tarihi == Ita dai Kambodiya wata ƙasa ce da ke kudu maso gabashin Asiya kuma ta na da jama'a da yawansu ya haura miliyan 13. Sunan babban birnin ƙasar Phnom Penh. Kambodiya ta samo asali ne daga daular Hindu da Buddha, wadda ta mulki yankunan Indonesiya da China tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 14. Yawancin ‘yan ƙasar Kambodiya mabiya addinin Buddha ne, amma kuma akwai musulmi da dama da chinese ‘yan asalin ƙasar, da yan asalin ƙasar Vietnam da kuma yan tsirarun yarurruka da ke zaune akan tsaunuka. Ƙasar Kambodiya na maƙwabtaka da ƙasashen Thailand a yammaci da kuma yamma maso arewa, Laos a arewa maso gabas da Vietnam a gabas da kudu maso gabas. A kudu tana fuskantar kogin Thailand. Siyasa a ƙasar Kambodiya ta kafu ne akan tafarkin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1993, kuma tsari ne da aka yi da ke da Sarki da kuma Firaminista, waɗanda wakilan jama'a ne ke zaɓansu. Firaministan ƙasar shi ne shugaban gwamnati, wadda ta ƙunshi jam'iyyu dabam-dabam, a yayin da kuma sarki shi ne shugaban ƙasa. Sarki ne ke naɗa Firaminista tare da shawara da kuma yardar majalisar ƙoli ta ƙasar. Firaminista tare da ministocin sa na da ikon zartar da doka a gwamnati, a yayin da alhakin tsara dokoki ya rataya ne akan majalisun dokoki da kuma ɓangaren masu zartar da dokar. A ranar 14 ga watan Oktoba, wata majalisa ta musamman mai wakilai 9, ta zaɓi Sarki Norodom Sihamoni, a wani tsari na zaɓe da aka yi cikin gaggawa, sati ɗaya bayan Sarki Norodom Sihanouk, ya ƙi amincewa. Zaɓen sarki Sihamoni ya sami albarkacin Firaminista Hun Sen da shugaban majalisar dokokin ƙasar, Norodom Ranariddh, waɗanda dukkan su wakilai ne a majalisar zaɓen sarki. An rantsar da sabon sarkin ne a ranar 29 ga watan Oktoba, a babban birnin Kambodiya, wato Phnom Penh. Masana'antun ƙasar Kambodiya dai sune na sutura, yawon shaƙatawa da kuma gine-gine. A shekara ta 2007, yawan baƙin da suka ziyarci ƙasar daga ƙasashen waje ya haura miliyan biyu. An gano mai da albarkatun ƙasa a ƙarkashin ruwan dake zagaye da ƙasar a shekara ta 2005, kuma idan aka fara zaƙulo waɗannan albarkatun ƙasa a shekara ta 2011, to ana ganin cewa kuɗin shigan da za a riƙa samu daga Man zai haɓaka arziƙin ƙasar ta Kambodiya [[ace:Kamboja]] [[af:Kambodja]] [[als:Kambodscha]] [[am:ካምቦዲያ]] [[an:Cambocha]] [[ang:Cambodia]] [[ar:كمبوديا]] [[arz:كامبوديا]] [[ast:Camboya]] [[az:Kamboca]] [[bar:Kambodscha]] [[bat-smg:Kambuodža]] [[bcl:Kambodya]] [[be:Камбоджа]] [[be-x-old:Камбоджа]] [[bg:Камбоджа]] [[bn:কম্বোডিয়া]] [[bo:ཁམ་པོ་ཛ།]] [[bpy:কম্বোডিয়া]] [[br:Kambodja]] [[bs:Kambodža]] [[bug:Kamboja]] [[bxr:Камбож]] [[ca:Cambodja]] [[ce:Камбоджа]] [[ceb:Cambodia]] [[ckb:کەمبۆدیا]] [[crh:Kamboçiya]] [[cs:Kambodža]] [[csb:Kambòdżô]] [[cv:Камбоджа]] [[cy:Cambodia]] [[da:Cambodja]] [[de:Kambodscha]] [[diq:Kamboçya]] [[dsb:Kambodža]] [[dv:ކެންބޯޑިއާ]] [[dz:ཀམ་བོ་ཌི་ཡ་]] [[el:Καμπότζη]] [[en:Cambodia]] [[eo:Kamboĝo]] [[es:Camboya]] [[et:Kambodža]] [[eu:Kanbodia]] [[ext:Camboya]] [[fa:کامبوج]] [[fi:Kambodža]] [[fiu-vro:Kambodža]] [[fr:Cambodge]] [[frp:Cambodg·e]] [[fy:Kambodja]] [[ga:An Chambóid]] [[gag:Kamboca]] [[gan:柬埔寨]] [[gd:Cambuidea]] [[gl:Camboxa - កម្ពុជា]] [[gn:Kamboja]] [[gu:કમ્બોડીયા]] [[gv:Yn Chamboyd]] [[hak:Kán-pu-chhài]] [[haw:Kamabodia]] [[he:קמבודיה]] [[hi:कम्बोडिया]] [[hif:Cambodia]] [[hr:Kambodža]] [[hsb:Kambodźa]] [[ht:Kanbòdj]] [[hu:Kambodzsa]] [[hy:Կամբոջա]] [[ia:Cambodgia]] [[id:Kamboja]] [[ie:Cambodja]] [[ilo:Cambodia]] [[io:Kambodja]] [[is:Kambódía]] [[it:Cambogia]] [[ja:カンボジア]] [[jv:Kamboja]] [[ka:კამბოჯა]] [[kk:Камбоджа]] [[km:ព្រះរាជាណាចក្រកម្ពុជា]] [[kn:ಕಾಂಬೋಡಿಯ]] [[ko:캄보디아]] [[ku:Kamboca]] [[kv:Камбоджа]] [[kw:Kamboji]] [[la:Cambosia]] [[lb:Kambodscha]] [[li:Cambodja]] [[lij:Cambògg-ia]] [[lmo:Cambogia]] [[ln:Kamboji]] [[lo:ປະເທດກຳປູເຈຍ]] [[lt:Kambodža]] [[lv:Kambodža]] [[map-bms:Kamboja]] [[mdf:Камбоджа]] [[mg:Kambodia]] [[mi:Kamapōtia]] [[mk:Камбоџа]] [[ml:കംബോഡിയ]] [[mn:Камбож]] [[mr:कंबोडिया]] [[ms:Kemboja]] [[my:ကမ္ဘောဒီးယားနိုင်ငံ]] [[na:Kambodja]] [[nah:Camboya]] [[nap:Cambogia]] [[nds:Kambodscha]] [[nl:Cambodja]] [[nn:Kambodsja]] [[no:Kambodsja]] [[nov:Kambodia]] [[oc:Cambòtja]] [[or:କମ୍ବୋଡ଼ିଆ]] [[os:Камбоджæ]] [[pa:ਕੰਬੋਡਿਆ]] [[pam:Cambodia]] [[pih:Kamboedya]] [[pl:Kambodża]] [[pms:Cambògia]] [[pnb:کمپوچیا]] [[ps:کمبودیا]] [[pt:Camboja]] [[qu:Kambuya]] [[rm:Cambodscha]] [[ro:Cambodgia]] [[roa-rup:Cambogia]] [[ru:Камбоджа]] [[rw:Kambodiya]] [[sah:Камбодьа]] [[scn:Camboggia]] [[sco:Cambodie]] [[se:Kampučea]] [[sh:Kambodža]] [[si:කාම්බෝජය]] [[simple:Cambodia]] [[sk:Kambodža]] [[sl:Kambodža]] [[so:Kambodiya]] [[sq:Kamboxhia]] [[sr:Камбоџа]] [[ss:IKhambodiya]] [[su:Kamboja]] [[sv:Kambodja]] [[sw:Kamboja]] [[szl:Kambodża]] [[ta:கம்போடியா]] [[te:కంబోడియా]] [[tg:Камбоҷа]] [[th:ประเทศกัมพูชา]] [[tk:Kamboçiýa]] [[tl:Cambodia]] [[tr:Kamboçya]] [[tt:Камбоҗа]] [[udm:Камбоджа]] [[ug:كامبوجا]] [[uk:Камбоджа]] [[ur:کمبوڈیا]] [[vi:Campuchia]] [[vo:Kambocän]] [[war:Cambodia]] [[wo:Kamboodi]] [[wuu:柬埔寨]] [[xal:Камбудин Нутг]] [[yi:קאמבאדיע]] [[yo:Kàmbódíà]] [[zh:柬埔寨]] [[zh-classical:柬埔寨]] [[zh-min-nan:Kampuchea]] [[zh-yue:柬埔寨]] All content in the above text box is licensed under the Creative Commons Attribution-ShareAlike license Version 4 and was originally sourced from https://ha.wikipedia.org/w/index.php?oldid=23126.
![]() ![]() This site is not affiliated with or endorsed in any way by the Wikimedia Foundation or any of its affiliates. In fact, we fucking despise them.
|