Difference between revisions 71431 and 157754 on hawiki{{databox}} [[File:Cambodia - Sihanoukville.jpg|thumb|kasar cambodiya]] Ita dai '''Kambodiya''' wata ƙasa ce da ke kudu maso gabashin [[Asiya]] kuma ta na da jama'a da yawansu ya haura miliyan 13. Sunan babban birnin ƙasar [[Phnom Penh]]. Kambodiya ta samo asali ne daga daular Hindu da Buddha, wadda ta mulki yankunan [[Indonesiya]] da [[Sin|China]] tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 14. [[File:Nature of Cambodia. Ream.jpg|thumb|tsaunukan kasar camboniya]] Yawancin ‘yan ƙasar Kambodiya mabiya addinin Buddha ne, amma kuma akwai musulmi da dama da chinese ‘yan asalin ƙasar, da yan asalin ƙasar [[Vietnam]] da kuma yan tsirarun yarurruka da ke zaune akan tsaunuka. Ƙasar Kambodiya na maƙwabtaka da ƙasashen [[Thailand]] a yammaci da kuma yamma maso arewa, [[Laos]] a arewa maso gabas da Vietnam a gabas da kudu maso gabas. A kudu tana fuskantar kogin Thailand. ==Siyasa==⏎ Siyasa a ƙasar Kambodiya ta kafu ne akan tafarkin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1993, kuma tsari ne da aka yi da ke da Sarki da kuma Firaminista, waɗanda wakilan jama'a ne ke zaɓansu. Firaministan ƙasar shi ne shugaban gwamnati, wadda ta ƙunshi jam'iyyu dabam-dabam, a yayin da kuma sarki shi ne shugaban ƙasa. Sarki ne ke naɗa Firaminista tare da shawara da kuma yardar majalisar ƙoli ta ƙasar. Firaminista tare da ministocin sa na da ikon zartar da doka a gwamnati, a yayin da alhakin tsara dokoki ya(contracted; show full) Masana'antun ƙasar Kambodiya dai sune na sutura, yawon shaƙatawa da kuma gine-gine. A shekara ta 2007, yawan baƙin da suka ziyarci ƙasar daga ƙasashen waje ya haura miliyan biyu. An gano mai da albarkatun ƙasa a ƙarkashin ruwan dake zagaye da ƙasar a shekara ta 2005, kuma idan aka fara zaƙulo waɗannan albarkatun ƙasa a shekara ta 2011, to ana ganin cewa kuɗin shigan da za a riƙa samu daga Man zai haɓaka arziƙin ƙasar ta Kambodiya {{Asiya}} {{DEFAULTSORT:Kambodiya}} [[Category:Ƙasashen Asiya]] All content in the above text box is licensed under the Creative Commons Attribution-ShareAlike license Version 4 and was originally sourced from https://ha.wikipedia.org/w/index.php?diff=prev&oldid=157754.
![]() ![]() This site is not affiliated with or endorsed in any way by the Wikimedia Foundation or any of its affiliates. In fact, we fucking despise them.
|